TAKAITACCEN TARIHIN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA DANGANE DA ABUN DA YA SHAFI NEMAN ILIMINSHI DA KUMA MALAMAN SHI.
An haifi Ash-Sheikh Albani Zaria ne a watan Rabiu Thani 1379 dai dai da 27 Sept 1960, a cikin garin Muciya Zaria, Sabon Garin Kaduna, Najeriya.
Malam ya taso tun yana yaro da son ilimi kamar yadda wani malamin shi ya siffanta shi da cewa: “Albaniy tun yana 'Karami da angan shi ina kaje; karatu, ina zaka; karatu, me kake yi; karatu, me ka gama; karatu.
Mahaifiyar shi mai Suna Saudatu ita ta fara bashi 'karfin guiwar karatun addini na musamman, domin itace wadda ta fara siyar da akuyar ta, ta bashi kudin ya siyo littafin Saheehu Muslim inshi na farko. Har ila yau mahaifiyarshi ta taba 'daukan shi tun yana 'karami ta kaishi gurin wasu malamai a cikin garin Kano domin su karantar dashi Karatun addini da zummar cewa 'danta ya zama Malami.
A 'bangaren karatun Al-Qur'ani; Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara karatun Allo ne a cikin anguwar mucciya dake Zaria. A inda ya sauke Qur'ani saukar Farko ruwayar warsh 'kira'ar Nafi'u a hannun Mallam Mato da Alarama Mallam Abubakar.
A 'bangaren Larabci kuwa Ash-Sheikh Albani Zaria ya halarci wani karatu na wata goma sha takwas (18 months) a 'karkashin wani tsarin karatu da marigayi Gaddafi ya kawo Nigeria, a 'karkashin Jagorancin jami'ar Libiya a shekara alif dubu 'daya da 'dari tara da tasa'in. Babban Malami, marigayi Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, shi ya danka musu takardar shedar kammala karatun, kuma sai da yaba Albani Zaria wata takarda na jinjinawa ta musamman.
Dangane da sauran karatuttukan addinin musulunci kuma. Ash-Sheikh Albani Zaria yayi karatu a hannun Malamai da dama anan gida Nigeria da kuma Saudiya.
Kadan daga cikin malaman da yayi karatu a hannun su anan gida Nigeria sun kasance kamar haka; Dr Aminuddeen Abubakar Kano (Mai makarantar Kwali), Ash-Sheikh Sani Yakubu Zaria, Shehu Umar (Malami ne a Jami'a), Alkali Mallam Haruna Ishaq Zaria. Daga bisani Ash-Sheikh Albani Zaria (Rahimahullah) ya tare a hannun wani mutumin india mai suna Dr AbdulRahim Muhammad Muslim Khan wanda malami ne dake koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Mallam Muhammad Muslim Khan ya karantar da Albani Zaria littattafai masu yawa. A bangaren ilimin hadisi wannan malami Muhammad Muslim Khan ya karantar da Ash-Sheikh Albani Zaria littafin tadriburra'wi da musdala'ul hadith. A bangaren sauran littattafai kuma wannan malami ya karantar da Albani littafin Sifatu-Salatin Nabiy da kuma littafin Sharhus- Sunnah na Alhafiz Al-Bagawiy.
Daga baya a lokacin da Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara kasuwanci yana samun kudi, malam ya kasance yakan sayi tiket na jirgi musamman dan yaje 'Kasar Saudiyya yayi karatu a matsayin shi na 'dalibi mai niman ilimi bawai a matsayinshi na 'dalibin jamiatul Islamiyya ba.
Mallam yayi karatu a gaban Dr Muhammad Amin dake jamiatul Islamiyya dake madina, a inda ya koyi 'kira'ar Qur'ani 'kira'a bakwai ruwaya goma sha hudu.
Mallam Ya yi karatu a gaban Sheikh Uthaimin karatu sosai musamman ta fannin ilimin tafseerin Al-Qur'ani mai girma.
Mallam yayi karatun Aqeeda karatu sosai a hannun Addoktur Assuhaimi da professor Ali Nasir Faqihi wadanda dukkaninsu malamai ne a jamiatul islamiyya dake madina Kulliyatud-Da'awa wa usuluddeen.
Mallam yayi karatu a wurin mallam Tuwaijiri wanda ke karantarwa a Daruul-Hadeethisil Khairiyya dake Saudiyya.
Mallam yayi karatu a wajen Sheikh Zarban Al-gamidy, wanda shi ne tsohon Bursar (shugaban 'bangaren kudi) a jami’ar Madina.
Mallam yayi karatu a hannun Sheikh Abdullahi Bn AbdulRahman Alu Bassam (mai littafin taysirul Allam).
Mallam yayi Karatu a gaban Professor Samir wanda 'dalibi ne na Sheikh Nasiruddeen Albani.
Mallam yayi karatu a hannun Muhammad ibn Ali ibn Adam Al Ethiopy wanda shi kuma mutumin 'kasar Ethiopia ne.
Akwai malaman jami’ar Madina da yawa wadanda malam yayi karatu a gaban su, amma ba’a matsayin shi na 'dalibi a jami’a ba, A’a, a matsayin shi na 'dalibi wanda ya kai kanshi koyon ilimi a wurin su.
Wannan shine takaitaccen tarihin malam abin da ya shafi ilimi a taqaice. Allah (SWT) muke roko da ya jikan Mallam ya kuma sa Aljannat Firdausi ce makomarsa.
(REFERENCES: KARATUN SHARHUS-SUNNAH MASU TAKEN MUQADDIMA G, K & L, MUQADDIMAR KARATUN SAHEEHU MUSLIM, KASET 'DIN 'KADDAMAR DA SASHEN KARATUN QUR'ANI, TAFSEER 91, JARIDAR ATTATBIQ WANDA TA RUWAITO HIRARSU DA KHALIFAN SHEIKH ALBANI ZARIA, DR ABDULRAFIU ABDULGANIYU, HIRAR TARHO NA DITV KADUNA 2001)

No comments:
Post a Comment