<<<<<ASALIN BOKO HARAM<>>>>>>
¤¤¤^^^^^A~NIGERIA^^^^^^¤¤¤¤¤
Wannan magana tadade a Arewacin Nigeria tun zamanin zuwan Turawa kasar Nigeria babu shakka sarakuna da malaman musulunci nawancen lokacin sunyi fada da Akidar boko, yadda haryakai awajensu bokon ma kanta haramunne, wannan yasa mafiyawan mutanen Arewa basu sha'awar karatun boko, duba da yadda ilimin bokon yazo musu tahanya Turawan mulkin mallaka, tayadda gabadaya Al'adar malam Bahaushe tasha banban da wannan tsari na turawan mulkin mallaka, ina tuna daga baya baya lokacin muna Primary harwata waqa abokanmu suke mana wadanda basa zuwa makarantar boko, "Dan boko bokoko awuta"
Wannan yasa mafi yawan iyayenmu basuyi karatun boko ba, dan haka yasa suke daukar yaransu suke turasu kasar gabas wato Maiduguri karatun Muhammadiyya ma'ana karatun Allo,
Sunyi hakanne duba da yadda tsarin karantarwar yazo wanda yake hade da rashin kunya da fitsara wacce tasabawa Al'adar malam Bahaushe, haka akai tatafiya, har zuwa 1987 lokacin da akai zaben shugaban kasa akasar Algeria inda 'yan uwa musulmi wadanda suke da kishin musulunci suka ci zaben shugaban kasa, ita kuma kasar Amurka data duba taga lallai idan tabari wadannan mutane sukecigaba da mulki awannan kasa akwai yiyuwar suyaqi kafirci aduniya, wannan yasa sukai maqarqashiya aka suke zaben, inada aka nada Gwamnatin riqon kwarya.
Wannan yasa suwadannan mutane sukai tawaye gawannan gwamnatin riqon kwaryar suka hana yin aiki awannan Gwamnati suka hana shiga gwamnatin hadaka, sukeita bada fatawowi sabanin shawarwarin da manyan malamai na duniya suka basu irinsu Nasuruddenul Albani da Bn Baz da su Uthaimin wannan yasa suke tara kudade masu yawa da makamai donsu yaki wannan Gwamnati ta riqon kwarya,
Daga baya suke watsu aduniya don yada wannan akida ta kyamar aikin Gwamnati ana haka suka hadu da Malam Yusif Agarin maiduguri.
Malam Yusif Mutumin kasar maiduguri Babar barene yanajin yaren Barbarci da Fullaci da Hausa Ranga dadau, kuma yayi karatun Qur'ani irin na Gardan taka ma'ana karatun Allo baitaba zuwa makarantar koyon Tajwid ba koyaje makaranta koyon Tafser amma Allah yabashi zalakar harshe wanda alokacin har yarike matsayin wakilin Zakzaky a Maiduguri,
Daga baya da'awar Sunnah tai tasiri akansa yashiga sunnah amma baya karatu wannan yasa yakeda zafin ra'ayi lokacin da Marigay Sheikh Ja'afar Mahmud Adam yafara Tafser amasallacin Dr. Ndimi malam Yusif yafara zuwa wannnan Tafser wannan shine zamanshi nafarko agaban Halka ta ilimi;
Daga nan sai yahadu dawani mutumin Kaduna dakuma Bashir Dan sudan wanda ya zauna akano yariqa kafirta dukkanin musulmi masuyin karatun boko, daga baya bayan suntattauna dasu Dr. Ahmad Bomba dasu Malam. Abba Adam Koki, ya tattara yanasa yanasa yakoma wani gari a jahar Niger wajejan Makwa, inda suka kafa gari maisuna Darul-salam
Malam Yusif ansamshe alokacin dayake ganiyarsa domin baya karatu kuma ga akidar gardan taka ta kyamar karatun boko, wannan yasa yakarbi wannan da'a takyamar aikin Gwamnati amma shi saiya sauya ainihin da'awar yamaida ita ta kyamar karatun boko,
yasami gudun mawar kudade da makamai daga wadancen mutane 'yan Algeria inda suka tsara Agendar guda uku 1)YAKAR MALAMAN SUNNAH 2)YAKAR WADANDA SUKAI MUSU TAWAYE 3)YAKAR GWAMNATI,
Daga nan Malam Yusif yakama wa'azi yana fassara wadansu ayoyi acikin Qur'ani dasukai magana akan Jihadi dakuma wadansu ayoyi dasukai magana akan Science karkumanta baiyi karatu maizurfi dazai dauki wadannan mas'aloli manyaba, amma haka yafara da'awar Boko Haramce hakan Aikin gwamnati ma Haramne,
Kadan daga cikin abubuwan da malam. Yusif yatabo wadanda sunfi karfinsa sune, Science dake cikin Qur'ani kamar guraren da Allah yake maganar kowacce halitta daga ruwa take, dakuma inda Allah yake bayanin Halittar dan Adam dakuma yadda sama da kasa suke ahade,
Dakuma bayanan Malam Ilimin kimiya wadan yake ganin sunsabawa ayoyin Qur'ani,
Bayan kuma manyan malaman musulunci na duniya sunyi Rubece rubece akan Science wanda baije yakarantaba,
Misali tun shekara 700 da suke wuce Ibn Qaiyumul-jauzi yarubata littafi wanda aka fassara da turanci mai suna (HELLING WITH THE MEDECINE IN THE PROPHET)
Hakanan wani bature dan kasar America mai suna Profeser Moris Orkala wanda malamin Science kwararre akan harkar bince, lokacin da yai bincike yagano cewar Asalin kowanne abu daga ruwa ne, sai akace masa aitun wajen shekara 1,000 dasuka wuce Qur'ani yabaina haka, yace akawo masa Qur'anin, bayan kawo masa yaga hakan bazai gamsheshiba, dan haka yatafi birnin Jeddah yazauna tsawon shekara 5 yana karantar harshen larabci sannan yakaranci Qur'anin daga baya yarubata wannan littafin,(THE QUR'AN AND MODERN SCIENCE COMPORTABLE OR INCOMPORTABLE)
Dan haka manyan malamai na musulunci harma wadanda ba musulmiba sunyarda cewar Qur'ani da Ilimin kimiyya ko Science basa cin karo da juna
TO irin wadannan Muhammad Yusif yake qoqarin tabbatarwa Alhalin baiyi karatunsuba, domin dukkan mas'alolin sunfi karfinsa,
Nanma wani malamine dan kasar India Mai suna SHABIR AHMAD yarubuta wani littafi maisuna (DEVELOPMENT SCIENCE AND TECNOLOGY IN ISLAMIC HISTORY)
Shima yai bayani sosai akan wannan mas'ala
Zanci gaba dakawo sauran litattafai dakuma litattafin da Dr. Zakir Naick yarubuta bayan Tattaunawarsu Da Dr. Wiliams
Insha Allah...............
No comments:
Post a Comment