Thursday, 5 June 2014

ANYA KUWA MUTUMIN BANZA ZAI YI IRIN WANNAN MUTUWAR?

Tsarki ya tabbata ga Allah! Idan ka kalli irin mutuwar da Ash-Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria yayi za kaga abun mamaki mai tarin yawa.

(1) A duk duniyar nan idan ka cire Al-Qur'ani mai girma babu littafin da yafi Saheehul Bukhari. A duk duniya idan ka cire Al-Qur'ani da Saheehu Bukhari babu littafin da yafi Saheehu Muslim. A duk duniya idan ka cire Al-Qur'ani da Hadisi babu littafin da yafi na gyaran zukata da Aqeeda.

Allahu Akbar! A safiyar ranar da malam yayi 'kaura daga da duniyar nan sai da ya karantar da littafin gyaran zuciya ('Darikatus-Salihina).

Allahu Akbar! A yammacin ranar da mallam yayi 'kaura daga duniyar nan sai da ya karantar littafin Saheehu Muslim.

Allahu Akbar! A daren ranar da mallam yayi 'kaura daga duniyar nan sai da ya karantar da littafin Saheehu Bukhari.

Kaga kena duka wadannan
littattafan guda uku masu daraja a duniyar musulunci sai da mallam ya karantar dasu a wannan ranar da ya rasu.

(2) Sanannen Abune cewa; Manzon Allah (S.A.W) yace idan ya kasance aikin karshen mutum a rayuwarshi ya kasance na alkhairi ne to ko shakka babu wannan mutumin 'dan Aljannah ne. Allahu Akbar! Malam ya dawo ne daga karatun saheehu Bukhari a masallacin Markazus-Salafiyya, yana hanyarsa ta komawa gida akazo aka yi mishi kisan gilla dashi da matarsa da 'dansa kamar yadda aka yima Sayyidina Ali (RTA) a yayin dawowar shi gida daga masallaci.

(3) Sanannen abune cewa manzon Allah (SAW) yace duk wanda aka kashe shi haka kawai bai jiba bai gani ba toh dukkannin zunubanshi sun koma kan wannan wanda yayi kisan. Allahu Akbar! Kashe mallam a kayi dashi da matarsa da 'dansa basu jiba basu gani ba wanda hakan yasa dukkannin zunubansu sun koma kan makisansu insha'Allah.

(4) Sanannen abune cewa Manzon Allah (SAW) yace dukkannin ran da kalmarta na 'karshe ta kasance kalmar shahada to sakamakon wannan ran shine Aljannat Firdausi. Allahu Akbar! Malam ya rasu ne yana furta LA'ILA HA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH (SAW).

Sannan malam ya samu yabon
mutane dayawa kuma a tarihin 'kasar zazzau ba'a taba ganin taron 'dan adam a wurin jana'iza ba irin taron jana'izar mallam . Wanda hakan ma alamace ta mutuwar mutanen kirki.

Dan Allah mutumin banza zaiyi
wannan mutuwar????

No comments:

Post a Comment